Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

RFI Hausa

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Radios: RFI Hausa

Catégories: Actualités et Politique

Écoutez le dernier épisode:

Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.
 

Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi  a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.

Épisodes précédents

 • 318 - Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi 
  Tue, 27 Feb 2024
 • 317 - Shiri na musamman kan marigayi Salissou Hamissou 
  Tue, 20 Feb 2024
 • 316 - Yadda al'adar auren Zaga ke shudewa tsakanin kabilar Sayawa a Najeriya 
  Tue, 13 Feb 2024
 • 315 - Yadda wasu abincin gargajiya na bahaushe ke barazanar bacewa 
  Tue, 12 Dec 2023
 • 314 - Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya 
  Tue, 14 Nov 2023
Afficher plus d'épisodes

Plus de podcasts actualités et politique français

Plus de podcasts actualités et politique internationaux

Autres podcasts de RFI Hausa

Choisissez le genre de podcast