Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

Radios: RFI Hausa

Catégories: Éducation

Écoutez le dernier épisode:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi.

A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami’a.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

Épisodes précédents

 • 356 - Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe 
  Tue, 27 Feb 2024
 • 355 - Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai 
  Tue, 20 Feb 2024
 • 354 - Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai 
  Wed, 31 Jan 2024
 • 353 - Gwamnatin Neja na shirin farfado da tsarin karatun makiyaya 
  Tue, 19 Dec 2023
 • 352 - Taimakon da kirkirarren Tabarau ke bai wa masu fama da matsalar raunin gani 
  Tue, 28 Nov 2023
Afficher plus d'épisodes

Plus de podcasts éducation français

Plus de podcasts éducation internationaux

Autres podcasts de RFI Hausa

Choisissez le genre de podcast