Kasuwanci

Kasuwanci

RFI Hausa

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Radios: RFI Hausa

Catégories: Économie et Entreprise

Écoutez le dernier épisode:

Shirin "Kasuwa akai Miki dole" na wanan mako tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Dosso dake Jamhuriya Nijar, yankin da ke kan iyaka da birnin Cotonou na Jamhuriya Benin inda jama'a suka shiga matsanancin halin tsadar rayuwa tare da kariyar tattalin arziki, sakamakon takun-kuman da Kungiyayoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka laftawa kasar, saboda Juyin mulkin da Sojoji sukayi.

A Ranar 9 ga Watan Octoba da ya wuce Jamhuriya Benin ta rufe iyakar dake tsakaninta da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, bayan matakin da Kungiya ECOWAS ko CEDEAO ta dauka bayan da sojoji suka karbe mulki Ranar 26 ga watan Yuli wajen hambarar da shugaban Mohamed Bazoum.

Jamhuriyar Bénin ta dauki matakin soke duk wata hulda cinikaya da gwamnatin sojin Nijar.

Wanan matakin dai ya janyo hauhawa farashin Kayan bukatun jama'a na yau da kullun tare da haifar da koma bayan tattalin arziki a wasu sassan kasar, masamman  yankin Dosso, jiha daya tilo a Nijar da ta yi iyaka da Bénin har tsawan kilimita 150 daga yammacin Kasar.

Épisodes précédents

 • 310 - Yadda rufe iyakar Benin ya haifar da tsadar rayuwa a Nijar 
  Wed, 22 Nov 2023
 • 309 - 'Yan Najeriya na cikin matsin tattalin arziki tun bayan janye tallafin mai 
  Wed, 15 Nov 2023
 • 308 - Yadda masu kiwon kaji a Najeriya ke rufe gonakinsu saboda tsadar kayan abinci 
  Wed, 01 Nov 2023
 • 307 - Yadda aka sake bude kasuwar Monday Market a jihar Borno 
  Wed, 25 Oct 2023
 • 306 - CISLAC ta horas da 'yan majalisun Najeriya kan muhimmacin haraji ga kasa 
  Wed, 18 Oct 2023
Afficher plus d'épisodes

Plus de podcasts économie et entreprise français

Plus de podcasts économie et entreprise internationaux

Autres podcasts de RFI Hausa

Choisissez le genre de podcast